Isa ga babban shafi

Kwantiragin Haaland bai sahale masa komawa Real Madrid ba- Guardiola

Kocin Manchester City, Pep Guardiola ya yi watsi da rahotannin da ke cewa akwai wata sadara da ke kunshe cikin kwantiragin dan wasan gaban kungiyar, Erling Haaland da ta ba shi damar komawa Real Madrid a kan farashi mai rahusa.

Mai horas da Manchester City Pep Guardiola
Mai horas da Manchester City Pep Guardiola AP - Rui Vieira
Talla

Kafafen yada labaran Spain sun jaddada a wannan makon cewa akwai wata jimla da ta bai wa Real Madrid damar sayen Haaland a bagas idan har ta na bukatarsa.

Sai dai Guardiola ya ce babu wata jimla mai kama da haka a cikin kwantiragin shekaru 5 da dan wasan ya kulla da Manchester City a lokacin da zai baro Borussia Dortmond.

Guardiola ya ce ba wannan maganar sai dai kawai jita jita da mutane suka saba yadawa.

Ko a wasan da Manchester City ta doka jiya laraba sai da Haaland ya ci kwallaye 2 wanda ya baiwa kungiyar nasara kan Copenhagen da kwallaye 5 da nema karkashin gasar cin kofin zakarun nahiyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.