Ciwon zuciya ya tilastawa matashin dan wasa Mwepu yin ritaya
Ciwon zuciya na gado ya tilastawa dan wasan Brighton Enock Mwepu mai shekaru 24, yin ritaya daga buga kwallo.
Wallafawa ranar:
Kulob din na Premier Ingila ya ce Mwepu zai kasance cikin matukar hatsarin kamuwa da cutar bugun zuciya idan ya ci gaba da taka leda.
A kwanakin baya ne Mwepu ya kamu da rashin lafiya a balaguron da ya yi da tawagar kasar Zambia zuwa kasar Mali.
Bai samu damar shiga atisaye ba bayan ya isa yammacin Afirka a watan da ya gabata kuma ya kwashe kwanaki hudu yana jinya a asibiti.
Mwepu ya yi gwaje-gwaje bayan komawar sa Ingila inda Brighton ta ce sakamakon na nufin zabin da ke gareshi yin ritaya kadai.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu