Griezmann ya kammala komawa Atletico Madrid bayan zaman aro
Atletico Madrid ta sayi dan wasan gaban Faransa Antoine Griezmann daga Barcelona zuwa shekarar 2026.
Wallafawa ranar:
Griezmann ya kasance dan wasa na shida mafi tsada a tarihi lokacin da ya koma Barca kan fam miliyan 108 a shekarar 2019.
Ya zura kwallaye 35 a wasanni 102 da ya bugawa Barcelona kafin ya koma Atletico a matsayin aro na shekaru biyu a farkon kakar wasan data gabata.
Dan wasan mai shekaru 31, ya zura kwallaye uku sannan ya taimaka an ci biyu a wasanni 11 da ya buga kawo yanzu.
Akwai yarjejeniya a cikin kwantiragin aron na Griezmann wanda zai sanya Atletico sayen dan wasan gaban kan kudi Yuro miliyan 40 idan ya buga fiye da mintuna 45 a cikin sama da kashi 50% na wasanninsu.
Griezmann zai buga wasansa na farko a matsayin dan wasan Atletico Madrid a hukumance da kungiyar Club Brugge a gasar zakarun Turai ranar Laraba.
Dan wasan da ya lashe gasar cin kofin duniya ta 2018 shi ne na hudu da ya fi zura kwallo a raga a tarihin Barcelona inda ya zura kwallaye 144 a wasanni 304 da ya yi a wasanni biyu, bayan ya koma kungiyar daga Real Sociedad a shekara ta 2014.
Griezmann ya taba lashe kofin Europa League da Spanish Super Cup da kuma Uefa Super Cup.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu