Isa ga babban shafi

Mbappe na duba yuwuwar barin PSG a wannan kakar

Dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe da alama alakarsa da Paris Saint-Germain ta fara tabarbarewa yayin da dan wasan ke son barin kungiyar a lokacin hunturu, in ji wani rahoto da MARCA ta fitar.

Kylian Mbappé, avançado francês do PSG.
Kylian Mbappé, avançado francês do PSG. © AFP - ALAIN JOCARD
Talla

Sai dai Real Madrid ba ta tunanin yiwuwar zawarcinsa, kamar yadda majiyoyin kulob din suka shaidawa wannan jarida.

Wannan abin mamaki ne, duba da yadda Mbappe ya rattaba hannu a kan kwantiragi da kungiyar a watan Mayun da ya gabata, inda ya zabi rashin zama dan wasa mai ‘yanci kuma ya kasance mai cikakken iko kan makomarsa.

A cewar MARCA, PSG ba za ta yarda ta sayar da Mbappe ga wasu kungiyoyi ba musamman Real Madrid, wanda hakan ke nufin Liverpool ta kasance tana da karfin gwiwa idan har wannan maganar ta zama gaskiya kuma PSG ta yanke shawarar karbar tayin dan wasan.

Real Madrid na ganin Mbappe ya ki amincewa da kulob din sau biyu a rayuwarsa kuma ba su da cikakken tabbacin ko halinsa na iya haifar musu da matsala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.