Isa ga babban shafi

Ukraine ta bukaci FIFA ta haramtawa Iran zuwa gasar cin kofin Duniya

Hukumar kwallon kafar Ukraine ta roki hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA da ta haramtawa Iran shiga gasar cin kofin duniya da za ta gudana a Qatar, gasar da za a faro a karshen wannan wata na Nuwamba a kuma karkare a watan gobe.

Filin da za a doka gasar cin kofin Duniya.
Filin da za a doka gasar cin kofin Duniya. AFP - KARIM JAAFAR
Talla

Bayan wani zama da kwamitin gudanarwa na hukumar kwallon kafar Ukraine ya gudanar ne, kasar ta aikewa FIFA bukatar kunshe a wata sanarwa, inda zargi Iran da bai wa Rasha makamai don taimakawa a mamayar da Moscow ke yiwa kasar.

Rokon hukumar kwallon kafar Ukraine ya zo kwanaki kadan bayan da Shugaban kungiyar Shakhtar Donetsk Sergei Palkin ya yi kira da a cire Iran, a kuma bai wa Ukraine din damar maye gurbinta a gasar ta bana.

Ukraine na sahun kasashen da suka rasa a gurbi a gasar ta cin kofin Duniya wadda a wannan karon za ta gudana a gaba ta tsakiya, yayinda Iran wadda ta samu gurbin ta ke fuskantar barazanar gaza zuwa gasar musamman bayan zarge-zargen da ke nuna hannunta a taimakon Rasha.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.