Isa ga babban shafi

Aston Villa ta lallasa Manchester United 3-1

Unai Emery ya fara horar da Aston Villa da kafar dama, inda  suka lallasa Manchester United da ci 3-1 a Villa Park.

Cristiano Ronaldo, dan wasan  Manchester United.
Cristiano Ronaldo, dan wasan Manchester United. © AFP - LINDSEY PARNABY
Talla

Masu masaukin bakin ba su taba doke Manchester United a gidansu ba  a gasar League tun bayan shekarar 1995, amma sai gashi a wannan wasa sun ci kwallaye 2, United babu ko daya, bayan mintuna 11 bayan da suka fara wasa da karsashi.

Leon Bailey ne ya fara cin kwallo a minti na 7 da fara wasa inda  da ya fasa bayan United kafin ya antaya wa maiu tsaron raga, David de Gea ita a raga.

Lammura sun dada yi wa Villa kyau bayan mintuna 3 kacal, a yayin da Lucas Digne ya saka wata kwallo ta bugun tazara daga yadi na 25.

Manchester United sun yunkuro, inda Luke Shaw ya samu ya ci musu kwallo daya, bayan da ta daki jikin Jacob Ramsey.

Amma Ramsey ya mayar da martani, inda bayanhutun rabin lokaci ya lafta wa United kwallo a raga, kuma a haka aka tashi wasa 3-1.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.