Isa ga babban shafi

Da yiwuwar a sayar da kungiyar Liverpool nan kusa- Rahoto

Da yiwuwar a fara cinikin kungiyar kwallon kafa ta Liverpool kowanne lokaci daga yanzu, bayan da wani rahoto ke cewa mamallakan kungiyar sun sanar da shirin fara sayar da hannayen jari.

Tawagar kwallon kafa ta Liverpool bayan dage kofin UEFA Super Cup a Istanbul.
Tawagar kwallon kafa ta Liverpool bayan dage kofin UEFA Super Cup a Istanbul. AFP/Ozan Kose
Talla

Wata sanarwar rukunin kamfanonin Fenway Sports Group FSG, da ya sayi kungiyar ta Liverpool a shekarar 2010 kan farashin fan miliyan dari 3, ta yi shelar neman masu zuba jari.

An dai yi amfani da mafi yawan kudin ne wajen biyan basussukan da bankuna ke bin kungiyar a wancan lokaci, sai dai a karshen shekarar 2017-2018 kungiyar ta samu ribar da ta kai fam miliyan 106 bayan biyan dukkanin haraji, wanda ke da nasaba da sayen wasu zaratan 'yan wasa.

Tun bayan lokacin da FSG suka karbi ragamar kungiyar shekaru 12 da suka gabata, kofuna takwas suka lashe, inda 6 daga ciki Jurgen Klopp ne ya lashe musu.

A shekara ta 2015 ne, aka damkawa Klopp aikin horas da kungiyar inda kuma ya taimaka wajen ganin kungiyar ta lashe kofin zakarun Turai da kofin gasar Firimiyar Ingila na farko a shekaru 30.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.