Isa ga babban shafi

Gerard Pique ya cimma jituwa da Shakira kan makomar 'ya'yansu

Dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Barcelona Gerard Pique da tsohuwar budurwarsa Shakira sun cimma matsaya kan wanda zai kula da ‘ya’yansu bayan rabuwar da suka yi.

Gerard Piqué na Barcelona da Budurwar shi Shakira
Gerard Piqué na Barcelona da Budurwar shi Shakira © Esports
Talla

An shafe kusan sa'o'i 12 ana tattaunawa don cimma matsaya kan lamarin, inda shahararriyar mawakiyar ‘yar asalin Colombian ke neman yaran su koma wurin ta a birnin Miami na kasar Amurka.

Shi kuma dan wasan mai tsaron baya na Barcelona ya nemi yaran sun zauna da shi a Barcelona har sai sun kammala karatunsu, maimakon sanya su wata sabuwar makaranta a kasar da su ke baki, sai dai Shakira ta yi nasara akan batun.

Bayan ganawar, lauyoyin bangarorin biyu sun tabbatar wa manema labarai cewa sun yi nasarar cimma matsaya akan lamarin duk da dai basu yi karin haske akan yadda yarjejeniyar za ta kasance ba sai nan gaba.

Ganawar ta gudana ne a gidan Shakira kuma bayan tafiyar lauyoyin, Pique ya dade a cikin gidan lamarin da ake ganin an fahimci juna a ganawar ta su.

A dai talatar nan ce Pique da ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo kafa zai buga wasansa na karshe a Barcelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.