Isa ga babban shafi

Gasar Zakarun Kudancin Amurka: 'Yan wasa 10 daga bangare 1 sun samu jan kati

An kori 'yan wasa goma na kungiyar Boca Juniors a wasan karshe na kofin zakarun kudancin Amurka da kungiyar Racing ta lashe, inda 'yan wasa shida ne kawai suka yiwa kungiyar saura a cikin fili.

Carlos Tevez da wasu 'yann wasan Boca Junior na Argentina.
Carlos Tevez da wasu 'yann wasan Boca Junior na Argentina. AFP/Archives
Talla

An sallami 'yan wasan kungiyar Boca Bakwai, ciki har da biyu da ke kan benci, a lokacin da Racing ta kasance a gaba da ci 2-1 yayin da aka dakatar da wasan.

Dokar wasanni dai ta haramta ci gaba da wasa a lokacin da wata kungiya ke da kasa da ‘yan wasa 7 a cikin fili.

Murnar da Carlos Alcarez ya yi  a gaban magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Boca ne ya haifar da rikicin, bayan da ya jefa kwallo a minti na 118.

Sakamakon rikicin da aka fara ne ya sanya alkalin wasa Facundp Tello ya kori Alcarez ta re da ‘yan wasan Boca 5, kafin nan dama an sallami ‘yan wasan su biyu a minti na 95.

Alkalin wasan Tello wanda dan asalin Argentina ne, na daga cikin ‘yan wasan da za su yi alkalanci a gasar lashe kofin duniya da za’a fara a ranar 20 ga wannan wata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.