Isa ga babban shafi

An yi waje da Arsenal a gasar Kofin Carabao

Arsenal ta fice daga gasar kofin Crabao na Ingila a daren Laraba,bayan da ta sha kashi 3-1 a hannun Brighton.

Kocin Arsenal, Mikel Arteta.
Kocin Arsenal, Mikel Arteta. POOL/AFP
Talla

Dan wasan gaba na Arsenal, Eddie Nketiah ne ya bude wasan da kwallo daya a cikin mintin a 20 daga yadi na 18.

Wannan kokari na Nketiah ya wargaje, bayan da mai tsaron ragar Arsenal Karl Hein, wanda wasansa na farko kenan ya fito har sai da ya janyo bugun daga kai sai mai tsaron raga, kuma tsohon dan wasan Arsenal din  Danny Welbeck ya buga ya kuma ci.

Brighton sun ci gaba da matsa wa Arsenal lamba, inda suka samu kwallo ta 2 ta hannun Kaoru Mitoma.

A cikin minti na 7, Tariq Lamptey ya kara dora Brighton a kan Arsenal, wasa ya zama 3-1, kuma a haka aka tashi.

Wannan sakamako na nufin cewa an fitar da Arsenal daga wannan gasa a zagaye na 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.