Isa ga babban shafi

Kocin Kamaru ya fidda sunayen 'yan wasan da za su fafata a kofin duniya

Bayan kammala wasan sada zumuncin da aka yi tsakanin Kamaru da Jamaica da aka tashi 1-1 a filin wasa na Omnisport da ke Yaonde, mai horas da tawagar ta Kamaru Rigobert Song ya fidda sunayen ‘yan wasa 26 da zasu wakilci kasar a gasar lashe kofin duniya da za’a yi a Qatar.

wasu manyan 'yan wasan Kamaru ba su samu sshiga jerin wadanda za su wakilci kasar gasar kofin duniya ba.
wasu manyan 'yan wasan Kamaru ba su samu sshiga jerin wadanda za su wakilci kasar gasar kofin duniya ba. ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

‘Yan wasan dai sun hada da masu tsaron raga uku da masu tsaron baya 7 da ‘yan wasan tsakiya 6 sai kuma masu buga gaba mutum 10.

Masu tsaron ragar dai sun hada da Anre Onana da Devis Epassy da kuma Ngapandouetmbu, a bangaren ‘yan wasan baya akwai Fai Collins da Nicolas Nkoulou da Enzo Ebosse da Olivier Mbaizo da Nouhou Tolo da J.C Castelletto sai kuma Christopher  Wooh.

Su kuwa ‘yan wasan tsakiya akwai Oum Gouet da Martin Hongla da Gael Ondda da Zambo Anguissa da Kunde Malkong da kuma Olivier Ntcham.

'Yan wasan da za su bugawa Kamuru gaba a babbar gasar kwallon kafa ta duniya sune V. Aboubakar da Bryan Mbeumo da J.P Nsame da Nkoudou da Moumi Ngamaleu da Toko Ekambi da Choupo-Moting da Souaibou Marou da Bassogog sai kuma Ngom.

Akwai manyan ‘yan wasan Kamaru da ba za su samu damar zuwa wannan gasar ba, irin su Joel Matip, Ngandeu da Ondoua, sai dai kuma an samu sabbin ‘yan wasa irin su Christopher Wooh da Souaibou Marou da suka samu gurbin halartar gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.