Isa ga babban shafi

Rauni zai hana wasu manyan 'yan wasa zuwa gasar kofin duniya ta bana

A dai-dai lokacin da ya rage kwanaki goma a fara fafatawa a gasar lashe kofin duniya ta farko da za’a yi a watan Nuwamba a Qatar, akwai manyan ‘yan wasan da ba za su samu damar halartar gasar ba sabida raunin da suke fama da shi.

Paul Pogba na cikin 'yan wasan da rauni zai hana su zuwa gasar cin kofin duniya.
Paul Pogba na cikin 'yan wasan da rauni zai hana su zuwa gasar cin kofin duniya. © getty images
Talla

Manyan ‘yan wasan da tuni aka rika aka tabbatar da rashin zuwar su gasar dai sune Paul Pogba da N'Golo Kante da kuma Mike Maignan dukkanin su ‘yan wasan Faransa ne da Timo Werner dan wasan Jamus da Diogo Jota dan wasan Portugal da Georginio Wijnaldum dan wasan Netherlands sai kuma Alexis Saelemaekers daga Belgium.

Sauran ‘yan wasan sun hada da Diego Carlos da Arthur Melo dukkanin su ‘yan wasan Brazil sai Ben Chilwell da Reece James su kuma ‘yan wasan England ya yinda Jesus 'Tecatito' Corona shi kuma daga Mexico.

Sai dai akwai manyan ‘yan wasa da suka samu rauni kuma ake tunanin za su iya halartar gasar idan har sun murmure kamar yadda ake bukata.

Daga cikin su akwai  Sadio Mane daga Senegal da Paul Dybala da Giovani Lo Celso ‘yan Argentina da Romelu Lukaku dan wasan gaban Belgium da Florian Wirtz dan wasan Jamus sai kuma  Kamaldeen Sulemana daga Ghana.

Sauran ‘yan wasan sun hada da Sardar Azmoun Iran da Raul Jimenez Mexico da Dusan Vlahovic Serbia da  Son Heung-min daga Korea ta Kudu da Yann Sommer Switzerland  da Ronald Araujo dan wasan bayan Uruguay sai  kuma Joe Allen daga Wales.

Tuni dai wasu kasashe irin su Brazil da Spain da Wales da Cameroon da dai sauran su, suka fidda sunayen ‘yan wasan da zasu wakilce su gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.