Isa ga babban shafi

Magoya bayan Manchester United sun caccaki Ronaldo

Magoya bayan Manchester United sun nuna goyan bayansu ga manajan klub din Erik ten Hag saboda kalaman rashin martabawa da Cristiano Ronaldo ya yi bayan wasan da suka yi nasara ranar Lahadi kan Fulham da 2 – 1.

Dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo
Dan wasan gaba na Manchester United Cristiano Ronaldo © AFP - LINDSEY PARNABY
Talla

Karo na biyu kenan a baya-bayan nan,maimakon Manchester United ta yi farin cikin samun nasara, sai batun dan wasan ya mamaye batun, kamar yadda aka gani a cikin watan Oktoba bayan sun doke Fulham da ci 2 -0 batun rashin amincewa a sauya shi a fili ya mamaye nasarar da suka samu.

Ronaldo mai shekaru 37 da burinsa na neman wata kungiya mai doka gasar zakarun Turai bai cika ba, yace sam baya ganin girman manajan Club din Ten Hag, bayan da ya zarge shi tare da wasu abokan wasansa da cin amanarsa, abinda yasa magoyan bayan kungiyar suka ruga Twitter suna cewa Man - U tafi karfin dan wasa daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.