Qatar 2022: Netherlands ta lallasa Senegal a gasar cin kofin duniya
Kwallaye biyu da aka zura dab da za a tashi a wasa, sun baiwa Netherlands nasara da ci 2-0 a kan zakarun Afirka Senegal a ranar Litinin, yayin da 'yan wasan Louis van Gaal suka fara buga gasar cin kofin duniya a Qatar da kafar dama.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
An zura kwallon farko a wasan ne cikin minti na 84 da farawa a rukunin A lokacin da dan wasan gaba Cody Gakpo ya jefa kwallon farko a ragar Senegal, kafin daga baya Davy Klaassen ya ci ta biyu a karawar.
Yayin da Senegal ta rasa tauraron dan wasanta a wasan, sakamakon rauni wato Sadio Mane, karawar da kasashen da ke rukunin A suka yi a farkon wasan an yi hasashen za a tashi kunnen doki babu ci.
Sai dai ana saura minti shida, dan wasan gaban PSV Eindhoven Gakpo ya yi dirar mikiya a gaban golan Senegal Edouard Mendy.
Sakamakon ya sa Netherlands ta zama ta daya a rukunin da Ecuador, wacce ta doke Qatar da ci 2-0 a wasan farko na ranar Lahadi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu