Isa ga babban shafi

Mai yiwuwa gasar kofin duniya ta karshe kenan da zan buga - Messi

Lionel Messi  yana cikin yanayi mai armashi a yayin da yake shirin tinkarar abin da yake kusan a matayin gasar cin kofin duniyarsa ta karshe.

Lionel Messi.
Lionel Messi. Pool via REUTERS - MIGUEL GUTIERREZ
Talla

Dan wasan mai shekaru 35 zai fafata a gasar kofin duniyarsa na 5 kenan da tawagar kwallon kafar Argentina, wadda za ta yi wasan farko tsakaninta da ta Saudi Arabi a yau Talata da karfe 10 agogon GMT.

Da wasan wanda sau 7 ya lashe kyautar gwarzon dan kwallon kafa ta Ballon d'Or bai taba  lashe kofin duniya ba.

A shekarar 2014 ne ma ya kusan lashe wannan kofi a gasar da aka buga a Brazil, inda Argentina ta yi rashin nasara a wasan karshe.

Messi ya ce ba mamaki wannan ita ce gasar cin kofin duniya ta karshe da zai buga, kuma dama ta karshe da zai yi amfani da ita wajen cimma muradinsa.

Duk da cewa ya lashe kofuna da dama a matakin kungiya, a shekarar da ta gabata ce kawai ya ci wa kasarsa kofi, inda ya taimaka wa kasarsa Argentina ta lashe kofn Copa America.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.