Japan ta casa kasar Jamus a gasar cin kofin duniya
Japan ta lallasa Jamus da ci 2-1 a gasar cin kofin duniya da suka buga a ranar Laraba, yayin da Takuma Asano ya ci kwallon a minti na 83 abin da ya jefa kasar da ta taba lashe gasar har sau hudu cikin dimuwa.
Wallafawa ranar:
Ilkay Gundogan ne ya farkewa Jamus a bugun daga kai sai mai tsaron gida kafin Ritsu Doan ya rama a minti na 75 da fara wasa, wanda ya baiwa Japan damar samun galaba a wasan.
Jamus za ta kara da Spain mai rike da kofin shekarar 2010 a wasanta na gaba, kuma abin da take nema shine samun galaba a kan kasar idan har tana son kaucewa ficewa daga wasan rukuni karo na biyu a jere a gasar cin kofin duniya.
Kafin fara wasan dai, yan wasan Jamus sun rufe bakunansu da hannun dama, da nufin zanga-zangar adawa da hana musu amfani da kambu mai dauke da launin alamar bakan gizo, wanda ke nuni da goyon bayan masu auren jinsi da hukumar FIFA ta yi.
Kyaftin-kyaftin na kaashen Turai bakwai sun yi shirin amfani wannan kambu a gasar cin kofin duniya a Qatar, amma kasar ta ba zata lamunci hakan ba.
Launin na bakan gizo an haramta amfani da shi a kasar ta Qatar da ta ware doka mai tsauri ga masu aikata auren jinsi.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu