Isa ga babban shafi

Qatar 2022: Kocin brazil na da kwarin gwiwar Neymar zai ci gaba da wasa

Kocin tawagar kwallon kafar Brazil, Tite ya ce yana da kwarin gwiwar cewa Neymar zai sake yin wasa gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022, bayan da rahotanni suka ce ya fara atisayen murmurewa, sakamakon raunin da ya samu a idon sawunsa a wasan da suka fafata da Serbia.

Neymar,a. lokacin da ya ji rauni a Qatar 2022.
Neymar,a. lokacin da ya ji rauni a Qatar 2022. AP - LAURENT GILLIERON
Talla

Brazil sun tabbatar da cewa ba zai buga wasansu da Switzerland a ranar Litinin ba, inda wasu majiyoyi suka ce akwai yiwuwar ba zai fafata a wasansu na 3 ba, wanda zasu kara da Kamaru a ranar 2 ga watan Disamba.

Akwai fargabar cewa raunin da Neymar ya ji a idon sawunsa, da kuma wadda dan wasan baya, Danilo ya ji sa zu hana su fafatawa a gasar har a Karkare ta, amma a jiya Lahadi, Tite ya ce dukkannin ‘yan wasan za su yi wasa kafin a Karkare gasar cin kofin duniya.

A cikin minti na 80 aka sauya Neymar a wasan da suka doke Serbia 2-0, amma sai daga baya aka bayyana cewa ya ji rauni a idon sawu, bayan da Nikola Milenkovic ya make shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.