Isa ga babban shafi

Qatar 2022: Ingila za ta kara da Senegal a zagaye na 2

Sakamakon nasarar da Ingila ta yi a kan Wales da ci 3 da 1, ta kuma haye saman teburin rukuninta, yanzu za ta hadu da Senegala a zagayen ‘yan 16.

Marcus Rashford a lokacin da ya ci wa Ingila kwallo a gasar kofin duniya ta Qatar 2022.
Marcus Rashford a lokacin da ya ci wa Ingila kwallo a gasar kofin duniya ta Qatar 2022. REUTERS - MARKO DJURICA
Talla

Ingila, a karkashin mai horarwa, Gareth Southgate dai na neman lashe kofin duniya ne a karon farko tun bayan da ta lashe a shekarar 1966.

Senegal ta samu nasarar hayewa daga matakin rukuni a karo na biyu kenan, bayan da ta yi nasara a kan Ecuador da ci 2-1 aTalata, lamarin da ya sa ta kamala a matsayi na biyu a rukuninsu na A.

Za a yi wanna wasa n a ranar Lahadi, 4 ga watan Disamba a filin wasa na Al Bayt da birnin Doha a  Qatar da karfe 7 agogon GMT.

Tawagar kwallon kafar Senegal dai na matsayi na 18 ne a duniiya, matsayi mafi kololuwa da wata tawagar kwallon Afrika ta taba samu.

Ta kuma lashe. kon nahiyar Afrika a karon farko a shkarar 2021, bayan da sau biyu tana kai wa wasan karshe amma ana doke ta a shekarun 2002 da 2019.

Wannan ne karon farko da tawagar Ingila da ta Senegal za su fafata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.