Isa ga babban shafi

Fifa ta bude shari'ar ladabtarwa akan Uruguay da 'yan wasanta hudu

Fifa ta bude shari'ar ladabtarwa a kan hukumar kwallon kafar Uruguay da 'yan wasa hudu kan abubuwan da suka aikata a wasansu na karshe na gasar cin kofin duniya da Ghana.

Wasan rukunin H da Uruguay ta doke Ghana a filin wasa na Janoub da ke kasar Qatar
Wasan rukunin H da Uruguay ta doke Ghana a filin wasa na Janoub da ke kasar Qatar REUTERS - JOHN SIBLEY
Talla

Uruguay ta doke Ghana da ci 2-0, amma duk da haka ta fice daga gasar, inda ta zo ta uku a bayan Koriya ta Kudu a rukunin H.

‘Yan wasan na Uruguay sun mayar da martani da kakkausar murya ga alkalin wasa sakamakon gaza samun bugun fanareti bayan da aka yi taho mu gama tsakanin Darwin Nunez da Alidu Seidu.

Jose Maria Gimenez da Edinson Cavani da Fernando Muslera da kuma Diego Godin duk suna fuskantar yuwuwar ladabtarwa saboda keta dokoki Fifa, sakamakon nuna rashin da’a ga alkalin wasa.

Hukumar FA ta Uruguay na fuskantar hukunci kan keta dokokin, da kuma wani abin da ya shafi nuna wariya.

Har ila yau Fifa ta bude shari'a kan hukumar kwallon kafa ta Serbia dangane da abubuwan da suka faru a lokacin da Switzerland ta doke su da ci 3-2 a wasansu na karshe na rukunin G.

Hukumar kwallon kafa ta duniya ba ta fayyace abubuwan da suka faru ba, amma an gaya wa magoya bayan Serbia a lokacin wasan da su daina nuna wariyar launin fata.

Tuni Fifa ta fara binciken Serbia bayan da tawagar ta rataya wata tuta mai cike da cece-kuce da ke nuna Kosovo a dakin hut una ‘yan wasanta kafin Brazil ta doke su a gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.