Isa ga babban shafi

Qatar 2022: Japan ta fice daga gasar cin kofin duniya

Croatia ta kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar cin kofin duniya sakamakon doke Japan da ci 3-1 a bugun fenareti bayan da aka tashi kunnen doki da ci 1-1 a wasan.

Dan wasan Japan Ritsu Doan kenan daga hagu tare da Kaoru Mitoma lokacin da suke murnar kwallon da aka zurawa Croatia.
Dan wasan Japan Ritsu Doan kenan daga hagu tare da Kaoru Mitoma lokacin da suke murnar kwallon da aka zurawa Croatia. AP - Eugene Hoshiko
Talla

Mario Pasalic ne ya zura kwallon da ta kai Croatia mataki nag aba a bugun daga kai sai mai tsaron gida, bayan da Ivan Perisic ya farkewa Croatia a minti na 55 da fara wasan, lokacin da Daizen Maeda ya ci wa Japan kwallon kafin a tafi hutun rabin lokaci.

Yanzu dai Croatia za ta kara da Brazil ko kuma Koriya ta Kudu a wasan dab da na kusa da karshe, wanda hakan zai bawa dan wasan tsakiyar real Madrid Luka Modric i ci gaba da kasancewa a gasar cin kofin duniya karo na hudu kuma mai yiwuwa na karshe.

Mafarkin Japan na zuwa zagayen ‘yan takwas ya gamu da cikas karon farko a tarihinta, wato irin abun da ya faru da kasashen Jamus da spain a matakin rukuni E da aka yi waje da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.