Isa ga babban shafi

Brazil, Faransa, Morocco na shirin fafatawa a matakin kwata-final

Manyan Kasashen duniya a bangaren kwallon kafa na shirin fafatawar da za’ayi a matakin kwata-final na gasar cin kofin duniyar dake gudana a Qatar, inda yanzu haka kungiyoyi 8 suka rage daga cikin 32 da suka samu damar shiga gasar. 

Filin wasa na Education City Stadium kenan lokacin da 'yan wasan Morocco ke marnar samun nasara akan Spain
Filin wasa na Education City Stadium kenan lokacin da 'yan wasan Morocco ke marnar samun nasara akan Spain REUTERS - WOLFGANG RATTAY
Talla

Daga cikin wadanda suka rage, akwai Brazil wadda ta taba lashe kofin har sau 5 da Faransa mai rike da kofin da Argentinar Lionel Messi da kuma Ingila da ita ma ta samu damar lashe kofin har sau 3. 

Sai kuma Morocco wadda ta kauda duk wata fatar da Spain ke da ita na lashe kofin, abinda ya bata damar zama kasar Afirka daya tilo da ta rage a gasar da kuma Portugal ta Cristiano Ronaldo wadda ta samu gagarumar nasara wajen kawar da Switzerland da ci 6-1, sai kuma Croatia da Netherlands. 

Jadawalin wasan ya nuna cewar a ranar juma’a mai zuwa, Croatia zata kara da Brazil, yayin da Argentina zata kara da Netherlands, sai kuma Morocco da zata fafata Portugal a ranar asabar, yayin da Ingila zata kece raini da Faransa. 

Ya zuwa wannan lokaci, ‘dan wasan gaban Faransa Kylian Mbappe ke sahun gaba wajen wadanda suka fi zirara kwallo a raga, inda ya jefa kwallaye 5, sai kuma Goncalo Ramos na Portugal da Alvaro Morata na Spain da Lionel Messi na Argentina da Marcus Rashford da Bukayo Saka na Ingila, sai kuma Olivier Giroud masu kwallaye 3-3. 

Sauran masu kwallaye 3-3 sun hada da Richarlison na Brazil da Eduador Valencia na Ecuador da Cody Gakpo na Netherlands. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.