Isa ga babban shafi

Ronaldo ya musanta batun komawa Al-Nassr ta Saudiyya

Cristiano Ronaldo ya musanta cewa ya amince ya koma wasa a kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr da ke kasar Saudiyya, a ganawar da aka yi da shi  bayan nasarar da Portugal suka samu a kan Switzerland a daren Talata.

Cristiano Ronaldo.
Cristiano Ronaldo. © LUSA - JOSE SENA GOULAO
Talla

Da aka tambaye shi a game da rade radin cewa zai koma wasa Al Nassr, Ronaldo ya ce sam babu gaskiya a cikin wannan maganar.

Kyaftin din Portugal din ba shi da kungiyar da yake yi wa wasa a yanzu haka, tun bayan da suka cimma matsaya da Manchester United a kan zai bar kungiyar a watan Nuwamba.

Rahotanni da suka fito daga Spain tun daga Litinin din nan sun ce Ronaldo zai fara wasa a kungiyar Al Nassr ta Saudiya, sakamakon amincewa da kwantiragin shekaru 2 da rabi da yayi da ita, wanda aka ce zai karbi abin da ya kai Yuro miliyan 200 duk shekara.

Lallai ba shakka Al Nassr ta yi kokarin dauko Ronaldo, inda ta yi tayi mai gwabi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.