Isa ga babban shafi

Abinda ya sa nake sumbatar mahaifiya ta bayan wasa - Hakimi

Wani abinda ke ci gaba da dauke hankalin mabiya kwallon kafa a gasar cin kofin duniyar dake gudana a Qatar, shine yadda ‘dan wasan Morocco, Achraf Hakimi ke rugawa wajen mahaifiyarsa yana sumbatar ta da zaran sun kammala wasa. 

Dan wasan Morocco da PSG kenan Achraf Hakimi
Dan wasan Morocco da PSG kenan Achraf Hakimi © Sport brief
Talla

‘Dan wasan kungiyar PSG dake kasar Faransa na daya daga cikin zaratan ‘yan wasan Morocco dake ci gaba da samun nasara a wasannin na Qatar, ganin yadda suka kawar da manyan kasashe irinsu Spain da Portugal. 

Hakimi na daga cikin wadanda suka taka gagarumar rawa wajen kai Morocco zuwa matakin wasan kusa da na karshe da zasu fafata a ranar Laraba da Faransa mai rike da kambun gasar. 

Sai dai bayan zama daya daga cikin tauraron ‘yan wasan Morocco, Hakimi na dauke hankalin ‘yan kallo da kuma masu bibiyar kasarsa a gasar, yadda da zarar an kammala wasa ya kan ruga wurin mahaifiyarsa domin sumbatarta a cikin yan kallo. 

Yayin da yake tsokaci akan wannan mataki da yake dauka, Hakimi yace iyayensa sun sadaukar da rayukansu wajen taimaka masa kaiwa matakin da yake yanzu, saboda haka ba zai yi watsi da su ba, abin da yasa yake alfahari da su koda yaushe. 

‘Dan wasan yace mahaifiyarsa tayi aikatau wajen kula da gidajen jama’a domin biya masa bukatu, yayin da mahaifinsa kuma yake sayar da kaya ne a titi domin samar musu abinda zasu ci. 

Hakimi yace wannan sadaukarwar da suka masa wajen aiki tukuru har ya kai shi matakin da yake yanzu, ba zai bashi damar juya musu baya ba, saboda haka yake alfahari da su koda yaushe. 

Ya zuwa wannan lokaci Hakimi mai shekaru 24 yayi nasarar bugawa wasu daga cikin manyan kungiyoyin kasashen Turai irin su PSG da Inter Milan da Borussia Dortmund inda ake bayyana shi a matsayin daya daga cikin fitattun yan wasan baya na duniya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.