Isa ga babban shafi

Qatar 2022: Morocco na kokarin hana Faransa sake lashe kofin duniya

Yau Kasar Faransa dake rike da kofin duniya zata fafata da Morocco wadda ke ci gaba da kafa tarihi a gasar dake gudana a Qatar, wajen kawar da manyan kasashen duniya domin samun gurbin zuwa wasan karshe da za’ayi a karshen mako. 

'Yan wasan PSG biyu da Achraf Hakimi na Morocco da Kylian Mbappé na Faransa zasu yi kokarin kare kambin kasashensu.
'Yan wasan PSG biyu da Achraf Hakimi na Morocco da Kylian Mbappé na Faransa zasu yi kokarin kare kambin kasashensu. © montage RFI - AP/Ebrahim Noroozi - Reuters/Lee Smith
Talla

Nasarar Faransa a karawar ta wannan Laraba zai bata damar kalubalantar Argentina a wasan karshe domin ganin ta koma da kofin gida, wanda zai zama shine irinsa na farko a cikin shekaru 60 da wata kasa zata lashe kofin sau biyu a jere. 

Masu sharhi

Wasu masu sharhi akan harkokin kwallon kafa na hangen Faransa a matsayin wadda ta fi zaratan ‘yan wasan da zasu iya taimaka mata samun nasara a karawar ta daren Laraba, yayin da wasu ke cewa ‘yan wasan Morocco abin tsoro ne ganin sai daya aka zirara musu kwallo a bugun finaretin bayan karin lokacit unda aka fara gasar ta Qatar. 

Shi kansa kaftin din Faransa Hugo Lloris ya gargadi abokan wasansa da kada suyi kasa a gwiwa lura da irin kokarin da Morocco keyi a gasar ta Qatar.  

Lloris yace kungiyar da ta doke Belgium da Spain da kuma Portugal abin tsoro ne saboda jajartattun ‘yan wasan da take da shi dake taimaka mata samun nasara. 

Fargabar fuskantar juna

Jagoran ‘yan wasan na Faransa ya kuma ce suna fargabar fuskantar juya musu baya daga tarin ‘yan kallon dake Qatar wadanda akasarinsu zasu goyi bayan Morocco. 

Mai horar da ‘yan wasan Morocco Walid Regragui wanda aka haifa a Paris, kana kuma yayi wasa a gasar kungiyoyin kasar ya bayyana kungiyarsa a matsayin wadda ke ci gaba da samun tagomashi. 

Regragui yace duk da nasarorin da kungiyarsa ta samu har yanzu suna da yunwar ganin sun samu nasara akan Faransa domin zuwa mataki na gaba da zai basu damar karawa da Argentina. 

Manajan yace babu dalilin da zai sa bayan zuwa wannan mataki ace basa mafarkin lashe kofin, lura da cewar kungiyar da tafi kowacce kokari ta Brazil ta koma gida. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.