Isa ga babban shafi

Qatar 2022: Morocco ta fice daga gasar cin kofin duniya

Faransa ta kawo karshen mafarkin Morocco a gasar cin kofin duniya yayin da kwallayen da Theo Hernandez da Randal Kolo Muani suka ci ya baiwa masu rike da kofin gasar, damar doke su da ci 2-0 a wasan daf da na karshe.

Tawagar 'yan wasan Faransa bayan sun fafata da Morocoo
Tawagar 'yan wasan Faransa bayan sun fafata da Morocoo REUTERS - HANNAH MCKAY
Talla

A minti na biyar ne Theo Hernandez ya zura kwallo ta farko a ragar Morocco sai kuma Randal Kolo Muani da ya kara ta biyu a minti na 79 da fara wasa.

Morocco, wadda ita ce ta farko a Afirka da ta taba kai wa zagaye na hudu na karshe a gasar cin kofin duniya, ta fafata ne duk da rashin manyan 'yan wasanta da suka samu rauni.

Wannan dai shi ne karo na hudu da Faransa za ta buga wasan karshe a gasar cin kofin duniya sau bakwai da ta taba fitowa, kuma suna fatan zama kungiya ta farko tun bayan Brazil shekaru 60 da suka wuce da ta rike kambun gasar sau biyu a jere, inda  za su kara da Argentina a filin wasa na Lusail ranar Lahadi.

Morocco ta kai wasan kusa da na karshe ne bayan ta doke Belgium a matakin rukuni sannan ta fitar da Spain da Portugal.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.