Isa ga babban shafi

Hukumar kwallon kafar Faransa tayi tir da masu nunawa 'yan wasanta bakaken fata kyama

Hukumar kula da kwallon kafar Faransa tayi Allah wadai da mutanen kasar da suka fito fili suna nunawa ‘yan wasan da suka wakilci kasar a gasar cin kofin duniya banbancin launin fata, sakamakon rashin nasarar da suka samu yayin karawarsu da Argentina. 

Olivier Giroud, Antoine Griezmann, Aurélien Tchouaméni tare da Kylian Mbappé, lokacin da suka koma kasarsu bayan kammala gasar cin kofin duniya a Qatar.
Olivier Giroud, Antoine Griezmann, Aurélien Tchouaméni tare da Kylian Mbappé, lokacin da suka koma kasarsu bayan kammala gasar cin kofin duniya a Qatar. REUTERS - SARAH MEYSSONNIER
Talla

Hukumar tace tana nazari domin daukar matakan shari’a akan irin wadannan mutanen da suka ci zarafin ‘yan wasan. 

Wannan mataki ya biyo bayan kuskuren da ‘yan wasa irinsu Kingsley Coman da Aurelien Tchouameni suka yi lokacin da suka barar da bugun daga kai sai mai tsaron gidan da ya baiwa Argentina damar lashe kofin. 

Ko a shekarar 2020 an samu irin wannan matsala bayan gasar cin kofin Euro, lokacin da bakaken ‘yan wasan Ingila suka barar da fenariti, abinda ya kaiga kai musu hare haren nuna wariyar jinsi a cikin kasar. 

Shugabannin hukumar kwallon kafar Faransa sun gabatar da sanarwa mai dauke da kakkausar furuci akan masu nunawa wadannan ‘yan wasa bakar fata kyama ta kafar sada zumunta. 

Hukumar kwallon kafar ta sha alwashin gabatar da korafi a gaban shari’a akan mutanen da suka gabatar da irin wadannan kalamai domin ganin an hukunta su. 

Tuni kungiyar Bayern Munich ta fito tana kare ‘dan wasanta Coman wanda shigarsa wasan ya sauya taka rawar Faransa da kuma taimaka mata wajen ganin ta farke kwallayen da Argentina ta zirara musu. 

Sanarwar kungiyar yace ba zasu bari nuna wariyar jinsi ya samu wurin zama a harkar kwallon kafa ba ko kuma a cikin al’umma. 

Jam’iyar adawar Faransa ta masu neman kawo sauyi ta bukaci hukumar kwallon kafar da ta tashi tsaye wajen daukar matakan shari’a akan lamarin, yayin da ministar daidaiton jama’a Isabelle Rome ta bayyana nuna kyamar a matsayin abinda ba zasu amince da shi ba. 

Ko a shekarar 2020, Kylian Mbappe ya fuskanci irin wannan kyama lokacin da ya barar da fenaritin da aka bashi a karawar da suka yi da Switzerland. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.