Isa ga babban shafi

Hukumar kula da gasar lig za ta sanar da ranar fara gasar NPFL a Najeriya

Hukumar kula da gasar lig ta kwallon kafar kwararru a Najeriya LMSC ta ce a Larabar nan za ta sanar da ranar da za a fara babbar gasar kwallon kafa ta kasar, wato Nigerian Professional League (NPFL) ta kakar wasan 2022/23.

'Yan wasan Lobi Stars da Adamawa United a Najeriya
'Yan wasan Lobi Stars da Adamawa United a Najeriya Daily Trust
Talla

Shugaban hukumar, Gbenga Elegbeleye, ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da manema labarai a birnin Abuja.

Wannan na zuwa ne bayan da hukumar ta yi watsi da ranar da masu ruwa da tsaki suka sanya tun da farko, a kokarin da suke na tilasta mata fara gasar a lokacin da suke so.

Hukumar ta shirya wani taro da shugabannin kungiyoyi 20 da ke cikin wannan gasar a Abuja, inda ake sa ran a cimma matsaya a kan abubuwa da dama.

Elegbeleye ya ce hukumaar za ta yi tsayuwar gwaman jaki wajen ganin kungiyoyi sun samu isassun kudade daga masu daukar nauyi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.