Isa ga babban shafi

Lionel Messi ya amince da bukatar PSG kan tsawaita kwantiraginsa

Rahotanni da kawo yanzu ba su kai ga tabbata ba a hukumance, sun ce Lionel Messi ya amince da tayin kara wa’adin yarjejeniyarsa da kungiyarsa ta PSG da tsawon shekara daya.

Dan wasan gaba na PSG, Lionel Messi.
Dan wasan gaba na PSG, Lionel Messi. © LUSA - MIGUEL A. LOPES
Talla

Wannan batu na zuwa ne duk da cewar tsohuwar kungiyar Messi wato Barcelona na son sake kulla yarjejeniya da shi, bayan da ya shafe shekaru 21 ya na taka mata leda.

A karshen kakar wasa ta bana yarjejeniyar Messi za ta kare da PSG, abinda ya sanya tun yanzu ake tofa albarkacin baki kan makomarsa.

Yanzu dai lokaci ne kawai zai fayyace inda Messi zai karkata, a tsakanin cigaba da zama a PSG, ko komawa kungiyar Inter Miami da ke Amurka, ko kuma komawa tsohuwar kungiyarsa ta Barccelona.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.