Isa ga babban shafi

An binne gawar gwarzon dan kwallon duniya Pele a Brazil

A ranar Talata ne aka gudanar da bikin binne gawar gwarzon dan kwallon duniya kuma dan kasar Brazil Pele, wanda ya rasu a ranar Alhamis 30 ga watan Disamban 2022, bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Lokacin da aka dauki akwatin gawar Pele kenan, zuwa makabartar Santos domin binne ta, ranar 3 ga watan Janairun 2023.
Lokacin da aka dauki akwatin gawar Pele kenan, zuwa makabartar Santos domin binne ta, ranar 3 ga watan Janairun 2023. AFP - CARL DE SOUZA
Talla

Sabon shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva na daga cikin wadanda suka halarci taron bankwana da gawar  Pele wanda ake ganin a matsayin dan wasan kwallon kafar da ba’a taba yin irin sa ba a duniya.

‘Yan siyasa da ‘yan kwallo da ma magoya bayan wasanni sunyi tururuwa wajen yin bankwana da gawar sa a kudancin birnin Santos inda nan ne ya buga mafi yawa daga cikin wasannin sa.

Kungiyar kwallon kafar Santos ta ce sama da mutane 200,000 ne suka halarci bikin bankwana da Pele.

Tsohon dan wasan wanda ya lashe kofin duniya sau uku, an binne shine a hawa na tara da ke makabartar Ecumenca Vertical yana kallon filin wasa na kungiyar Santos.

A yayin kewayen bankwana da aka yi da shi, akwatin gawar Pele ya wuce ta gaban gidan da mahaifiyar sa mai shekaru dari ta ke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.