Isa ga babban shafi

Al Nassr za ta mutunta hukuncin dakatarwar wasanni 2 kan Ronaldo

Kungiyar kwallon kafa ta Al Nassr a Saudi Arabia ta tabbatar da shirin mutunta hukuncin hukumar kwallon kafar Ingila kan sabon dan wasan da kungiyar ta saya Cristiano Ronaldo game da haramcin wasanni biyu da ke kansa.

Sabon dan wasan gaba na Al Nassr Cristiano Ronaldo.
Sabon dan wasan gaba na Al Nassr Cristiano Ronaldo. AFP - FAYEZ NURELDINE
Talla

Wani jigo a Al Nassr ya shaidawa AFP yau juma’a cewa tauraron na Portugal mai shekaru 38 ba zai taka leda a wasanni biyu da kungiyar za ta doka nan gaba ba, domin mutunta hukuncin.  

Tun a watan Nuwamba ne dai, hukumar FA ta dakatar da Ronaldo a wasanni biyu saboda samunsa da laifin jifan wani magoyin bayan Everton da wayar salula lokacin da ya ke shirin daukar hotonsa bayan rashin nasarar Manchester United hannun Everton a Goodison Park.

Har zuwa yanzu dai Al Nassr ba ta yiwa Ronaldo rijista ba, kasancewar kungiyar ta zarta adadin ‘yan wasa 8 sa hukumar kwallon kafar Saudiya ta sahale mata saye daga ketare duk kaka.

Zuwa yanzu dai Al Nassr ta sayi ‘yan wasan da yawansu ya kai 9 daga ketare ciki har da Ronaldo da ta sayo kan yuro miliyan 200 bayan dan wasan gaban na Portugal ya raga gari da Manchester United ana tsaka da gasar cin kofin Duniya.

Kwantiragin dan wasan mai shekaru 38 zai kaishi har zuwa watan Yunin 2025.

Yanzu haka dai Al Nassr na bukatar raba gari da dan wasa guda gabanin baiwa Ronaldo damar samun gurbi a Club din yayinda ake jita-jitar yiwuwar kungiyar za ta rabu ne da Jaloliddin Masharipov don samun gurbin yiwa tauraron na Portugal da ya lashe Ballon d’Or sau 5 rijista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.