Isa ga babban shafi

Gareth Bale ya sanar da yin ritaya daga kwallon kafa

Kyaftin din Wales Gareth Bale ya sanar da yin ritaya daga buga kwallo yana da shekaru 33 bayan ya taka rawar gani ga kasarsa.

Dan wasan gaban Wales Gareth Bale kenan.
Dan wasan gaban Wales Gareth Bale kenan. AFP/Archives
Talla

Dan wasan da ya fi kowa taka leda a kasar da ya buga mata wasanni 111 ya sanar da matakin da ya dauka a shafukan sada zumunta.

Bale, wanda ya lashe gasar zakarun Turai sau biyar tare da Real Madrid, za a iya cewa shi ne mafi kyawun dan wasan kwallon kafa da Wales ke alfahari da shi.

Gareth Bale wanda haifaffen dan Cardiff ne, ya fara wasan shi a babbar kungiya daga Southampton zuwa Tottenham Hotspur da Real Madrid kafin ya koma Los Angeles.

Ya kasance wanda ya yiwa kasarsa bajinta sosai yayin da suka kai ga gasar Euro 2016 da 2020 kafin ya jagoranci Wales a gasar cin kofin duniya ta farko tun 1958 a Qatar a 2022.

Wales dai ta fice daga gasar a matakin rukuni, bayan da rashin nasarar da ta yi a hannun Ingila shi ne wasan karshe na Bale.

Bale ya koma Southampton ne lokacin yana makaranta kuma ya fara taka leda a Saints yana dan shekara 16 a watan Afrilun 2006.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.