Isa ga babban shafi

Southampton ta fitar da Manchester City daga gasar cin kofin Carabao

Kungiyar Southampton ta yi bazata wajen fitar da Manchester City daga gasar cin kofin Carabao a jiya Laraba. 

'Yan wasan Southampton.
'Yan wasan Southampton. AFP
Talla

Bayan fafatawar mintuna 90 dai Southampton ta lallasa City da kwallaye 2-0 a filin wasa na Saint Mary. 

Wani abu da ya dauki hankali a wasan na jiya shi ne yadda City ta gaza samun damar yunkuri kwakkwara domin jefa kwallo a ragar Southampton, duk da cewar ita ke da mallakin maki 73 na rike kwallo a hannunta. 

Dukkanin manyan ‘yan wasan City da suka hada da Kevin de Bruyne, Erling Haaland, Phil Foden sun buga wasan na ranar Laraba, amma hakan bai hana su ficewa daga gasar ta Carabao ba. 

A halin yanzu Southampton za ta kara ne da Newcastle a zagayen kusa da na karshe, ranar 24 ga watan Janairu, yayin da kuma Manchester United za ta fafata da Nottingham Forest duk a ranar guda. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.