Isa ga babban shafi

Wane ne zai ji kunya tsakanin Ronaldo da Messi?

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi da suka dade suna hamayya da juna za su sake yin arangama a fafatawar da kungiyoyinsu biyu za su yi a Saudiya a ranar Alhamis mai zuwa.

Cristiano Ronaldo da Lionel Messi
Cristiano Ronaldo da Lionel Messi © Arabian Business
Talla

Wasan na sada zumunta shi ne na farko da Ronaldo zai fara buga wa sabuwar kungiyarsa ta Al-Nassr da ke Saudiya kuma tuni ta ayyana shi a matsayin kaften.

Ana sa ran PSG wadda yanzu haka ke ran-gadi a yankin gabas ta tsakiya za ta sanya Lionel Messi a karawar, lamarin da zai farfado da dadaddiyar hamayyarsa da Ronaldo.

Watakila wannan karawa za ta kasance ta karshe tsakanin zaratan 'yan wasan biyu da suka shafe tsawon shekaru 12 suna lashe kyautar Balon d'Or a tsakaninsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.