An sanya kungiyar kwallon kafa ta Everton a kasuwa
Kwanaki kadan bayan sallamar kocinsu Frank Lampard, mai kungiyar Everton, Farhad Moshiri ya sanya club din a kasuwa, inda ya ke neman akalla fam miliyan 500.
Wallafawa ranar:
A halin yanzu dai Everton ta na matsayin ta biyun karshe ne a teburin gasar Firimiya Ingila, bayan da ta buga wasanni 10 ba tare da samun nasara ba.
Jaridar The Guardian da ke Birtaniya, ta rawaito cewa attajirin Ba-Iraniye kuma dan Birtaniyar na shirin siyar da kungiyar ne sakamakon sukar da ya ke sha tare da sauran shugabannin club din daga magoya bayansu a makonnin baya-bayan nan.
Ya zuwa yanzu masu aniyar sayen kungiyar da dama sun gabatar da bukatarsu su, koda ya ke ba a kai ga bayyana daidaikunsu ba.
A halin da ake ciki kuma, wasu taurarin ‘yan wasa na kungiyar ta Everton, irin su Anthony Gordon da Amadou Onana sun tsallake zuwa atisaye a kokarinsu na ficewa daga kungiyar.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu