Isa ga babban shafi

Nijar za ta hadu da Algeria, Senegal da Madagascar a wasan gab da karshe na gasar CHAN

Gasar cin kofin Afirka ta ‘yan wasan cikin gida da ake kira CHAN da kasar Algeria ke karbar bakonci na gab da kawo karshe, inda a yau talata ake shirin doka zagayen kusa da na karshe tsakanin Algeria mai masaukin baki da jamhuriyar Nijar da karfe 4 sai kuma Senegal da Madagascar da karfe 8 . 

Kasashen 4 suka rage a gasar wadda Algeria ke daukar nauyi.
Kasashen 4 suka rage a gasar wadda Algeria ke daukar nauyi. © CAF on line
Talla

Wannan dai shi ne karon farko da kasashen Madagascar da Nijar suka samu tikitin shiga gasar cin kofin Afrika ta CHAN kuma suka iya kaiwa wannan mataki. 

Madagascar ta lallasa Mozambique da kwallaye 3 da 1 a Constantine yayinda Nijar ta doke Ghana wadda ta iya kaiwa wasan karshe na gasar har sau biyu inda ta zura mata kwallaye 2 da nema a Oran.

Wannan nasara ta Nijar da Madagascar ta basu damar shiga sahun 'yan hudun karshe da za su fafata a karawar ta yau, gabanin fitar da biyun da za su barje gumi a wasan karshe.

Babu wanda ya yi hasashen Nijar da Madagascar za su iya kaiwa wannan matsayi a gasar da aka fara ranar 13 ga watan Janairu. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.