Isa ga babban shafi

Liverpool ta yi nasara karon farko cikin 2023 bayan doke Everton

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool Jurgen Klopp ya ce yanzu ne ‘yan wasansa suka doka wasa kamar yadda aka sansu, bayan nasararsu ta doke Everton da kwallaye 2 da nema yayin haduwarsu ta jiya litinin a Anfield.

Wannan ne karon farko da Liverpool ta yi nasara a wasanta cikin shekarar.
Wannan ne karon farko da Liverpool ta yi nasara a wasanta cikin shekarar. AP - Peter Byrne
Talla

Liverpool wadda ke fama da rashin sa’a, bata iya nasara ko da a wasa day aba cikin shekarar nan yayinda ta ke ganin mafi munin koma baya tun bayan fara jan ragamarta da Jurgen Klopp ya yi.

Sai dai nasarar ta jiya da taimakon kwallaye daga Mohamed Salah a minti na 36 da kuma Gakpo a minti na 49 jim kadan bayan dawowa daga hutun rabin lokaci sun baiwa kungiyar damar doke babbar abokiyar dabinta ta cikin gida.

Itama dai Everton duk da yadda ta faro wannan kaka da nasara biyo bayan damka ta a hannun Sean Dyche sakamakon korar Frank Lampard, wanda ya kaisu ga nasarar doke Arsenal jagorar teburin na Firimiya yanzu haka ta na matsayin ‘yan ukun kasan teburi ne.

A cewar Klopp nasara a wasan na jiya ya samar musu da kwanciyar hankali lura da halin da suke ciki.

Yanzu haka dai Liverpool din ta dawo ta 9 a teburin firimiyar ta Ingila da maki 32 bayan doka wasanni 21.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.