Isa ga babban shafi

Arsenal da doke Everton da kwallaye 4 da nema

Da yiwuwar shan kayen Arsenal hannun Manchester City har gidanta ya karawa tawagar kwarin gwiwar tunkarar kofin gasar ta Firimiya a bana kamar yadda mai horarwa Mikel Arteta ya yi hasashe a wancan lokaci.

'Yan wasan Arsenal yayin murnar lashe zabe.
'Yan wasan Arsenal yayin murnar lashe zabe. © AFP - JUSTIN TALLIS
Talla

Tun bayan waccan rashin nasara dai daya kai ga kufcewar jagorancin teburi daga hannun Gunners anga yadda kungiyar ta koma turbar lashe wasanni gida da waje.

Bayan nasarar Arsenal ya doke Everton da kwallaye 4 da nema a daren jiya laraba yanzu tawagar ta Arteta na da tazarar maki 5 ne tsakaninta da City da ke matsayin ta biyu a teburin na Firimiya.

Nasarar ta jiya, ita ce ta 3 a jere da Arsenal ta yi tun bayan shan kayenta hannun City da kwallaye 3 da 1 inda yanzu haka ake da sauran wasanni 13 gabanin Karkare kaka.

Dama dai a jawabin Arteta bayan shan kayen Arsenal a hannun City, Manajan ya bayyana cewa a lokacin ne ya samu kwarin gwiwar cewa zai iya lashe kofin na Firimiya a bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.