Isa ga babban shafi

Neymar zai tafi hutun jinyar watanni hudu - PSG

Hukumomin gudanarwar Paris Saint-Germain ta kasar Faransa, sun fitar da sanarwar cewa dan wasan Brazil Neymar zai tafi hutun jinya, har tsawon watanni uku zuwa hudu.

Dan wasan PSG da Brazil kenan Neymar tare da Messi
Dan wasan PSG da Brazil kenan Neymar tare da Messi AFP - GEOFFROY VAN DER HASSELT
Talla

Sanarwar ta ce za a yi wa dan wasan aiki a kafarsa, bayan rauni da ya samu.

Neymar wanda ya samu raunin a ranar 19 ga watan Fabrairu, yayin wasan su da Lille a gasar Ligue 1, ta kasar Faransa, a ‘yan shekarun nan ya sha fama da ciwo a kafarsa ta dama.

Kulob din na Faransa ya ce likitoci sun bayar da shawarar a yiwa dan wasan aiki a wani asibiti da ke Doha, babban birnin kasar Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.