Isa ga babban shafi

Antonio Conte ya dawo daga hutun jinya - Tottenham

Kocin Tottenham Antonio Conte ya ce likitocin sun damu matuka game da lafiyarsa amma yanzu yana cikin koshin lafiya sosai, yayin da ya koma kungiyar domin ci gaba da horaswa.

Kocin Tottenham kenan Antonio Conte
Kocin Tottenham kenan Antonio Conte AFP/File
Talla

Conte, mai shekaru 53, wanda ya sha fama da ciwon mafitsara har ta kai ga an yi masa tiyata a watan jiya, ya koma Spurs inda ya jagoranci wasanni biyuy, said ai kuma ya gaza jagorantar kungiyar wasanni hudu, inda ya koma Italiya domin karasa murmurewa.

Zai dawo fagen daga dai abin da rahotanni ke cewa yanzu haka, domin jagorantar kungiyarsa a wasan da za ta kara da AC Milan a ranar Laraba.

Lokacin da ya tafi hutun jinya dai, Tottenham ta doke Chelsea da West Ham, amma Sheffishiped United ta fitar da su daga gasar FA kuma a ranar Asabar din da ta wuce ne suka sha kashi a hannun Wolves a gasar Premier.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.