Isa ga babban shafi

Babu alaka tsakanin makomata da wasan mu da Bayern Munich- Mbappe

Dan wasan gaba na PSG Kylian Mbappe ya yi ikirarin cewa nasara ko akasinta a wasan da za su doka da Bayern Munich yau laraba, ba shi zai fayyace makomarsa a fagen tamaula ba.

Dan wasan gaba na Faransa da ke taka leda da PSG Kylian Mbappe.
Dan wasan gaba na Faransa da ke taka leda da PSG Kylian Mbappe. REUTERS - DYLAN MARTINEZ
Talla

PSG dai na ci gaba da fuskantar matsin lamba bayan shan kaye da kwallo 1 mai ban haushi har gidanta a hannun Bayern Munich yayin haduwarsu a zagayen farko na wasan cikin kofin zakarun Turai rukunin kungiyoyi 16.

Yau laraba ake shirin doka zagaye na 2 na wasan tsakanin kungiyar ta PSG da Bayern wadda ke da tarihin lashe kofin na zakarun Turai har sau 7.

PSG wadda har zuwa yanzu ba ta taba lashe kofin na zakarun Turai ba, duk da zunzurutun kudin da ta zuba wajen sayen manyan ‘yan wasa, kacokan ta dogara ne ga irin rawar da Mbappe zai taka a wasan nay au, bayan da ya zo a matsayin sauyi yayin haduwar bangarorin biyu a watan jiya.

Yayin wancan wasa dai Kingsley Coman ne ya zura kwallo 1 tilo ga tsohuwar kungiyar tasa da ta baiwa Munich nasara kwatankwacin wadda ya zura a wasan karshe na gasar da kungiyoyin 2 suka hadu a 2019.

Sai dai Mbappe wanda ke matsayin dan wasa mafi zura kwallo a PSG da kwallaye 21 cikin wannan kaka, ya ce baya tunanin makomarsa karkashin gasar zakarun Turai ta dogara ne ga wasan na yau.

PSG dai za ta doka wasan na yau ba tare da ‘yan wasa irin Neymar Junior ba, yayinda Kyaftin Marquinhos da Nordi ke fama da rashin lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.