Isa ga babban shafi

Arsenal: Arteta ya ce dole sai Gabriel Jesus ya cancanci gurbi a tawagarsa

Mai horar da ‘yan wasan Arsenal, Mikel Arteta   ya bayyana dawowar Gabriel Jesus  matsayin wani karin kwarin gwiwa ga tawagarsa, sai dai ya yi kashedin cewa dole ne dan wasan ya dage don ganin ya samu gurbi a yayin da tawagar ke kokarin lashe kofin gasar Firmiyar Ingila.

Gabriel Jesus, dan wasan Arsenal.
Gabriel Jesus, dan wasan Arsenal. © AFP
Talla

Arsenal ta maido da tazarar maki 5 da take bai wa Man City a bayan da ta lallasa Fulham da ci 3-0 a ranar Lahadi, kwallayen da ta samu ta hannun Gabriel, Gabriel Martinelli da Martin Odegaard.

Leandro Trossard ya taimaka har sau 3 an ci kwallaye kafin daga bisani aka sauya shi da Gabriel Jesus a cikin minti 13 na karshen wasan.

Karo na farko Kenan Jesus ke fafata wa  Arsenal a gasar Firimiyar Ingila tun bayan da ya samu rauni a gwiwarsa a watan Nuwamban shekarar da ta gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.