Ten Hag ya ce na'urar VAR ba ta kyautawa
Kocin Manchester United, Erik ten Hag ya caccaki yadda aka yi amfani da na’urar VAR, mai taimaka wa alkalin wasa, bayan da aka bai wa Casemiro jan kati a karo na 2 tun da ya fara wasa a kungiyar.
Wallafawa ranar:
An bai wa dan wasan jan katin ne bayan da ya rafke Carlos Alcaraz a wasan da United ta buga canjaras babu ci da Southampton a ranar Lahadi, bayan da mai kula da ‘na’urar VAR, Andre Marriner ya shawarci alkalin wasa Anthony Taylor da ya duba na’urar.
Hukuncin ya fusataTen Hag ainun, musamman yadda ya ga cewa a ranar Asabar, dan wasan baya na Leicester, Ricardo Pereira bai samu jan kati ba, duk da cewa ya yi wa dan wasan Chelsea Joao Felix irin wannan duka.
Akwai ma inda Ten Hag ya ke ganin kamata ya yi a ba tawagarsa bugun daga-kai-sai-mai-tsaron raga, wato a lokacin da ya ke ganin Armel Bella-Kotchap ya taba kwallon da Marcus Rashfod ya bugo a cikin da’ira ta 18.
Kocin na United ya ce abin takaici ne ganin yadda na’urar ke yanke mabanbanta hukunci a kan laifuka iri guda.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu