Isa ga babban shafi

Sama da mutane miliyan daya da rabi suka nemi sayen tikitin wasan Argentina da Panama

A karon farko tun bayan lashe kofin Duniya da aka gudanar a Qatar, tawagar Argentina za ta buga wasan sada zumunci da Panama a ranar Juma’a.

Tawagar Argentina da ta lashe Kofin Duniya da aka yi a Qatar a shekarar 2022.
Tawagar Argentina da ta lashe Kofin Duniya da aka yi a Qatar a shekarar 2022. REUTERS - CARL RECINE
Talla

Wasan da za’a yi a babban filin wasa na Monumental da ke Buenos Aires wanda ke daukar ‘yan kwallo dubu 83, mutane miliyan daya da rabi ne suka nemi tikitin kallon wasan, kuma a cikin sa’oi biyu aka saida tikiti dubu 63 da aka warewa ‘yan kallo.

Haka nan hukumar kwallon kafar Argentina ta sanar da cewar akwai manema labarai dubu dari da 30 da suka nemi izinin daukar wasan duk da ya ke wurin da aka tanada don su bai wuce 344.

Tawagar Argentina na samun goyon baya yadda ya kamata a Buenos Aires, domin ko a lokacin kewayen nuna kofin duniya da kasar ta lashe a bara, sama da mutane miliyan biyar ne suka fito kan titunan birnin don taya murna.

Kyaftin din tawagar Lionel Messi na daga cikin ‘yan wasan da za su buga wasan na ranar Juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.