Isa ga babban shafi

Amurka na neman dan wasan Najeriya Balogun ya sauya sheka zuwa kasar

Kocin rikon kwarya na Amurka Anthony Hudson ya ce ana tattauna wa da Folarin Balogun kan dan wasan ya sauya sheka zuwa kasar.

Folarin Balogun kenan, da yanzu haka ke zzaman aro a Reims daga Arsenal.
Folarin Balogun kenan, da yanzu haka ke zzaman aro a Reims daga Arsenal. © ESPN
Talla

Dan wasan mai shekaru 21 an haife shi ne a Amurka, inda iyayensa suka kasance 'yan asalin Najeriya, amma kuma ya tashi a Ingila, don haka zai iya buga wa kowacce daga cikin wadannan kasashe ukun wasa.

Balogun, wanda ke zaman aro a kulob din Reims na Faransa daga Arsenal, ya buga wa Ingila wasa a kungiyoyin matasa hudu daban-daban.

Ya fice daga tawagar Ingila ta ‘yan kasa da shekara 21 a wannan makon saboda rauni da yake fama da shi.

Balogun ya ci wa Reims kwallaye 17 a gasar Ligue 1 a bana kuma kwallaye biyu ne kacal tsakanin sa Kylian Mbappe da Jonathan David.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.