Modric ya fara tattaunawa da Al-Nassr ta Saudiya
Dan wasan tsakiya na kungiyar Real Madrid Luka Modric ya yi tattaki zuwa Saudiya don tattaunawa da kungiyar Al-Nassr inda tsohon abokin wasan sa Cristiano Ronaldo ya ke.
Wallafawa ranar:
Talla
Wannan na zuwa ne gabanin yunkurin da ake na ganin dan wasan ya koma buga wasa a gasar Saudi Pro League.
Kungiyar ta Al-Nassr na shirin dauko dan wasan na Croatia, wanda ya koma Real Madrid daga Tottenham kan kudi Euro miliyan 35 a shekarar 2012.
Tun bayan komawar sa Madrid, dan wasan ya samu nasarar lashe kofuna 22 a kungiyar da kuma kyautar Ballon d’Or.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu