Isa ga babban shafi

Fitaccen dan wasan Real Madrid zai tafi hutun jinya na tsawon makonni

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta damu matuka cewa babban dan wasanta kuma mai tsaron raga wato Thibaut Courtois na iya zaman jinya har na tsawon wata guda bayan ya samu rauni a wasan da kasar Belgium ta doka.

'Yan wasan Real Madrid na murnar lashe kofin UEFA Super Cup da aka yi tsakanin Real Madrid da Eintracht Frankfurt a Helsinki, a ranar 10 ga Agusta, 2022 - Real Madrid ta lashe wasan da ci 2-0.
'Yan wasan Real Madrid na murnar lashe kofin UEFA Super Cup da aka yi tsakanin Real Madrid da Eintracht Frankfurt a Helsinki, a ranar 10 ga Agusta, 2022 - Real Madrid ta lashe wasan da ci 2-0. © AFP - JAVIER SORIANO
Talla

Golan ya samu raunin ne a wasan da Belgium ta doke Sweden da ci 3-0 a ranar Juma’a, wasan farko kenan na neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai na 2024 kuma lokacin da ya ya bar sansanin Belgium ya koma Madrid ne.

A cewar kafar yada labarai ta kasar Sipaniya, kungiyar kwallon kafar ta La Liga na fargabar cewa raunin zai iya sa Courtois yayi jinya na tsawon makonni uku zuwa hudu, inda aka ce dan wasan ya samu matsalar tsoka ne.

Real Madrid za ta karbi bakuncin Chelsea a Bernabeu ranar 12 ga watan Afrilu kafin su kara da juna a karawa ta biyu ranar 18 ga Afrilu a Stamford Bridge.

Watan Afrilu ya kunshi muhimman wasanni ga kakar Real Madrid saboda ba wai kawai za ta buga wasan zagaye na gaba na gasar zakarun Turai ba, za ta kara da abokiyar hamayyarta Barcelona a wasan kusa da na karshe na Copa del Rey.

Shugabannin kungiyar, za su damu da yadda wannan raunin zai iya shafar kakar wasan su amma, zai zama labari mai dadi ga magoya bayan kungiyar kwallon kafa ta Chelsea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.