Al Nassr ta sallami kocinta kasa da shekara guda bayan kama aiki
Kungiyar Al Nassr da ke Saudiya ta sallami kocinta dan Faransa Rudi Garcia, a ranar Alhamis
Wallafawa ranar:
Cikin sanarwar da ta fitar, Al Nassr ta ce ta raba gari da kocin ne bayan fahimtar juna da suka yi akan cewa matakin ne mafi dacewa a yanzu.
A watan Yulin da ya gabata Al Nassr ta kulla yarjejeniya da Garcia, mai shekaru 59, kuma ya bar kungiyar ne yanzu haka ta na kan matsayi na biyu a gasar kwallon kafa ta Saudiya maki uku tsakaninta da abokiyar hamayyarta Al Ittihad.
Garcia ya taba horas da kungiyoyin Lille da Marseille da kuma Lyon a kasarsa Faransa, ya kuma shafe shekaru biyu da rabi yana horar da kungiyar AS Roma a Italiya tsakanin shekarar 2013 zuwa 2016.
A karkashin tsohon kocin ne Al Nassr ta kulla yarjejeniya da Cristiano Ronaldo a watan Disamba kan yarjejeniyar biyansa sama da Yuro miliyan 400 a tsawaon shekaru biyu.
Ya zuwa yanzu Ronaldo ya ci wa kungiyar ta sa kwallaye 11 a wasanni 12 da ya buga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu