Isa ga babban shafi

An janyewa Juventus hukuncin rage maki 15 na saba ka'idan cinikin 'yan wasa

An janye hukuncin ragewa Juventus maki 15 kan cinikin musayar 'yan wasa da aka zarge ta a baya.Kotun kolin wasannin ta Italiya (CONI) ta amince da daukaka karar da Juventus ta yi kan hukuncin da aka yanke mata ranar Alhamis.

Alamar kungiyar kwallon kafar Juventus.
Alamar kungiyar kwallon kafar Juventus. © AFP Archives
Talla

Yanzu dai kotun ta bada umarnin a sake sabon shari'a a kotun wasanni ta hukumar kwallon kafar Italiya FIGC.

Da wanann mataki Juventus ta tashi daga matsayi na bakwai zuwa na uku a teburin gasar Seria A, wadda ta fitar da AC Milan mai rike da kofin gasar daga gurbin zuwa gasar zakarun Turai.

A binciken da aka yi, klub din ta saba ka’idar kashe kudade, don kare kimanin Yuro miliyan 90 tsakanin shekarar 2018 zuwa 2020.Baya ga hucin rage maki, an kuma hukunta shugabannin kulob din na wancan lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.