Isa ga babban shafi

Castellanos ya kafa tarihin shekaru 75 bayan jefa kwallaye 4 a ragar Madrid

Dan wasan gaba na Girona Valentin Castellanos ya zura kwallaye hudu da kungiyar ta yi raga-raga da Real Madrid mai rike da kambin gasar La Liga, a fafatawar da suka yi  ranar Talata da 4 -2.

Dan wasan gaba na Girona Valentin Castellanos ya zura kwallaye hudu da kungiyar ta yi raga-raga da Real Madrid. 25/04/23
Dan wasan gaba na Girona Valentin Castellanos ya zura kwallaye hudu da kungiyar ta yi raga-raga da Real Madrid. 25/04/23 REUTERS - ALBERT GEA
Talla

Castellanos shi ne dan wasa na farko a cikin sama da shekaru 75 da ya ci kwallaye hudu rigis a ragar Madrid a wasan La Liga tun daga shekarar 1947, lokacin da Esteban Echaverria ya ci wa Real Oviedo kwallaye biyar a ragar Madrid.

Dan kasar Argentina Castellanos, mai shekaru 24, na matsayin aro ne daga New York City.

Yanzu haka Real na biye ne da Barcelona dake saman teburi da tazarar maki 11.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.