Isa ga babban shafi

Arsenal na da kwarin gwiwar lashe kofin firimiyar bana- Arteta

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Arsenal Mikel Artete ya jaddada cewar suna dab da lashe gasar firimiyar Ingila bayan nasarar kwallaye biyu da nema da suka yi a a kan Newcastle a karshen mako.

Mai horas da kungiyar Arsenal Mikel Arteta
Mai horas da kungiyar Arsenal Mikel Arteta AP - Kirsty Wigglesworth
Talla

Arsenal wadda ke jagorantar teburin gasar a baya, a yanzu ta koma mataki na biyu, inda ta ke bin Manchester City da tazarar maki daya, duk da dai akwai ban-bancin wasa daya da Arsenal ta yi akan City, amma sai dai Artete ya ce ba za su hakura ba har sai anje karshen kaka.

Arteta ya ce ya yi farin ciki da irin rawar da kungiyar sa ta taka a karawar da suka yi da Newcastle da ke mataki na uku, wanda ake kallo a matsayin ramuwar gayya ganin a kakar da ta gabata rashin nasarar da suka yi a hannun Newcastle din ce ta hana su halartar gasar zakarun Turai.

Arsenal na da ragowar wasanni uku a gasar Firimiyar bana, wanda ta ke ganin nasarar lashe su zai iya cika mata fatan ta na lashe gasar idan har City ta yi rashin nasara a sauran wasannin ta hudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.